Wata kotu a Jakarta ta daure wani malamin addinin musulunci Abu Bakar Bashir daurin wata talatin a gidan kaso saboda hannunsa a harin bama-bamai a Bali a shekarar dubu biyu da biyu amma ta wanke shi daga zargin kai wani harin bam kan otel a shekara ta dubu biyu da uku. Magoya bayan malamin dan shekaru sittin da shida sun yi kabbara a kotun bayan da aka fadi hukuncin a inda shi kuwa malamin ya bayyana hukuncin da rashin tarbiyya. Ya kuma zargi Amurka kan wannan hukunci amma ya nemi magoya bayansa da su guji tada fitina. Alkalai biyar da suka yi shari’ar sun ce malamin ba kai tsaye ya ke da hannu a kan harin ba amma shi ya bayar da umarnin kai shi.
Akalla mutane dari biyu da biyu yawanci masu yawon shakatawa ‘yan kasashen waje ne aka halaka a harin na Bali. Bashir wanda aka zarga da laifin jagorantar wata kungiyar ‘yan ta’adda ta Jemaah Islamiyah an daure shi wata talatin a yau Al-hamis amma za a kwashe wata goma sha daya da ya yi yana jiran yanke hukunci. Sai dai alkalan sun ce babu isasshiyar shaida kan hannun Bashir a harin shekara ta dubu biyu da uku wadda aka kai kan otel din Marriott da ke Jakarta.
Hukuncin dai ya gaza daurin shekara takwas da mai gabatar da kara ya nema ya kuma jawo kushen Amurka. ‘’Muna girmama ‘yancin tsarin shari’ar Indonesiya kuma mun yi murna da hukuncin da aka yi wa wannan dan ta’adda amma ganin irin nauyin laifinsa munji haushin irin gajeren daurin da aka yi masa,’’ in ji Max Kwak mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Jakarta.
Ita kuwa Australiya wadda ta yi asarar ‘yan kasarta guda tamanin da takwas a harin na Bali ta ce ta so ta ga Bashir ya shafe shekaru da dama a gidan yari ta kuma ce za ta mika kukanta ga hukumomin Indonesiya. Amma ita kuwa Sidney Jones ta kungiyar International Crisis cewa ta yi gabatar da karar ce ba ta da karfi abinda ya jawo wannan gajeran daurin. Ta kuma ce wannana ba zai sa a ce Indonesiya ta gaza a kan yaki da ta’addaci ba. Ta ce, ‘’ ba na zaton cewa wannan hukunci zai zama wani mizanin auna dagewar gwamnatin Indonesiya kan yaki da ta’addanci ina ga a sauran abubuwa da wasu mutane ana kokari matuka.’’
Indonesiya ta gabatar da sama da mutane talatin saboda hannunsu a harin Bali kuma an yankewa uku hukuncin kisa. An dai kama Bashir ne jin kadan bayan harin Balin amma an kasa samun shaidar da za ta tabbatar da cewa shi dan ta’adda ne kuma shugaban kungiyar Jemaah Islamiyah wadda ake zargi da kai hare-hare a kudu maso gabashin Asiya. A maimakon haka an dai same shi ne da laifin karya dokokin shige da fice. Bayan zaman kason wata goma sha takwas an sake kama shi ne a watan Afrilu kan wasu zarge-zargen ta’addanci. Lauyoyinsa sun ce za su daukaka kara.