Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin harkokin wajen larabawa sun nemi ficewar Syria daga Lebanon - 2005-03-04


Ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa sun yi taro a Alkahira don share fagen taron kolin kungiyar a wani lokaci cikin wannan watan a Algeriya. Kodayake wannan batu ba ya cikin ajandar taron amma ministocin sun shafe ranar suna tattaunawa kan ci gaba da zaman dakarun Sham a Lebanon.

Ministocin kasashen Larabawan sun nuna goyon bayansu ga Sham din amma sun nemi da ta janye dakarunta daga Lebanon. Ministocin sun kuma nemi da Sham ta aiwatar da dukkanin yarjejeniyar alif da dari tara da tamanin da tara na janye dukannin dakarunta daga Lebanon. Kasar Sham na shirin aiwatar da yarjejeniyar janyewar sai dai ta sanya wasu sharudda. Wani jami’in kungiyar kasashen Larabawan da ba ya son a ambaci sunansa ya fada cewa ita dai Sham na bukatar dawo da tattaunawar zaman lafiya da Isra’ila kafin ta janye dakarunta daga Lebanon din.

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Amr Moussa ya ce ana kokarin shawo kan abinda ya kira manyan matsaloli don samun mafita. Sauran jami’an kasashen Larabawan sun ce ana kokarin sausata matsin da ake yiwa Sham. Sham dai na samun matsi daga cikin gida da kuma kasashen waje kan sai ta janye dakarunta kimanin dubu goma sha hudu daga Lebanon. A ranar Litinin firaministan Lebanon mai samun goyon bayan Sham Omar Karami ya bayyana saukarsa daga kan mulki bayan jerin zanga-zanga a Beirut babban birnin kasar.

A alif da dari tara da tamanin da tara wasu shugabannin kasashen Larabawa suka tsara wani shirin janyewar dakarun Sham zuwa kan iyakar Lebanon daga gabas daga nan kuma sai janyewar ta gaba daya ta biyo baya. Jami’an gwamnatin Sham har da shi kansa shugaba Bashar al-Assad sun bayyana burinsu na janyewa daga Lebanon sai dai ba su fadi lokacin da za a fara janyewar ba. Su kuwa jami’an Lebanon a Alkahira sun ce Lebanon na son ci gaba da dangantaka da Sham wadda ta mamaye siyasar kasar tun sama da shekaru goma da suka wuce. Sai dai taron bai samu halartar ministocin kasashen Sham da Lebanon ba. Shi da ministan harkokin wajen Sham Faruk al-Shara na tare da shugaba Assad wanda ke ziyara a Saudi-Arabiya don tattaunawa da jami’an kasar kan halin da ake ciki a Lebanon. Shi kuma ministan harkokin wajen Lebanon mai barin gado Mahmud Hammud ya tura wani jami’in diflomasiyya ne ya wakilce shi a taron na Alkahira. Ministocin kasashen Larabawan sun kuma tattauna kan shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdin da kuma irin ci gaban da ake samu bayan zaben Iraqi.

Ana sa ran taron shugabannin kasashen Larabawa na kwana biyu wanda za a fara a ranar ashirin da biyu ga wannan watan a Alges zai biyo bayan wannan taron ministocin.

XS
SM
MD
LG