Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar majalisar Iraqi za ta fara zama a makon gobe - 2005-03-07


‘Yan siyasar kasar Iraqi sun ajiye makon gobe ya zama lokacin da zababbiyar majalisar dokoki ta farko a kasar cikin wannan zamani za ta fara zamanta. Daya daga cikin manyan ayyukan da ke gabanta shine zabar firaministan da zai kafa sabuwar gwamnati.

Tattaunawa tsakanin manyan kungiyoyin siyasa uku har yanzu ba ta fitar da wata yarjejeniya ba amma jami’ai sun ce ‘yan majalisar za su sake taro a ranar sha shida ga watan Maris ko da ma ba wata yarjejeniya. Gamayyar jam’iyyun mabiya Shia da suka samu dan karamin rinjaye a zaben watan Janairu na son Ibrahim al-Jaafari a matsayin firaminista amma kuma firaministan gwamnatin rikon kwarya Iyad Allawi wadanda magoya bayansa suka samu kujeru ‘yan kalilan na shige da fice don ganin ya rike matsayinsa.

Sha shida ga wannan wata na Maris rana ce da ake bikin tuna kai hari da makamai masu guba kan garin Kurdawa na Halabja. Dakarun tsohon shugaba Saddam Hussein na Iraqi sun halaka mutane dubu biyar a wannan harin na shekarar alif da dari tara da tam,anin da takwas. A kuma wani labarin, a yau Litinin ne ‘yan tawaye suka kashe akalla sojojin Iraqi biyar a birnin Baquba da ke kudancin kasar sannan kuma wani harin bam din mota ya halaka ‘yan sanda guda biyu.

XS
SM
MD
LG