Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamandan sojan Amurka ya yi tir da dokar Sin kan Taiwan - 2005-03-09


Sabon kwamandan dakarun Amurka a yankin Pacific, Admiral William Fallon ya bayyana damuwa kan sabuwar dokar hana ballewa daga kasa da majalisar dokokin Sin za ta kafa a mako mai zuwa. A maganarsa ta farko kan wannan batu tun lokacin da ya karbi jagorancin wannan babbar runduna kusan kwana goma da suka wuce Amiral Fallon ya gayawa kwamitin harkokin soja na majalisar dattijan Amurka cewa yana daya daga cikin abinda ya ba mahimmanci, kara nazarin wannan batun Sin da Taiwan da kuma abinda Amurka za ta iya yi don rage zullumi.Ya kuma ce wannan doka da Sin za ta kafa na sanya masa damuwa.

‘’Abin takaici ne wannan doka da Sin ke kokarin kafawa na hana ballewa kamar yadda suka kira ta, tana da matsi kuma za ta basu dama bisa doka na daukar matakin soja. Kuma ina ga wannan matakin ba shi da amfani ga kokarinmu na rage tararrabi tsakanin Sin da Taiwan ‘’ in ji Admiral Fallon. Sabuwar dokar ta bayar da dama ga Sin da ta dauki mataki koda bana lumana ba wajen tabbatar da hadewa da Taiwan idan hakan ya zama dole. Sin dai ta ce tana da damar yin amfani da karfi don cimma wannan hadewa to amma wannan sabuwar doka za ta bayar da damar yin hakan.

Taiwan ta balle ne daga Sin a lokacin juyin-juya halin ‘yan kwaminis na alif da dari tara da arba’in da tara kuma tun shekaru da dama tana ikirarin gwamnati mai cin gashin kai. Amma a ‘yan shekarunnan maganar cin gashin kan Taiwan ta kasance wani babban batu a tsibirin. Amurka dai ta ce ta amince da China guda daya kuma bata amince da ‘yancin gashin kan Taiwan ba kuma tana son a sasanta ta hanyar tattaunawa. Amurka na da dangantakar tattalin arziki mai karfi da Sin tana kuma da tsohuwar dangantakar tsaro da Taiwan. Duk wani harin sojan Sin kan Taiwan ka iya jawo martani daga sojan Amurka. Admiral Fallon ya ce yana aiki da sauran kananan kwamandojinsa don ganin rundunar sojan Amurka a Pacific ta rage zaman dar-dar tsakanin Sin da Taiwan.

Kwamandan ya kuma gayawa ‘yan majalisar dattijan cewa rundunar na da karin karfin iko a yankin kuma sojan Amurka na sama dana ruwa dana kasa za su iya tabbatar da karfin sojan kasar Amurka a yankin kuma ka iya aiwatar da duk wani aiki da aka sa su yi a duk fadin yankin.

XS
SM
MD
LG