Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na bukatar sansanonin soja a Romaniya da - 2005-03-10


Kwamandan dakarun Amurka a Turai Janar James Jones ya ce Amurka a shirye take ta fara tattaunawa da sababbin mambobin kungiyar kasashen tsaro ta NATO Romaniya da Bulgeriya kan ajiye dakarun Amurkan a cikin kasashensu.

Janar Jones ya gayawa kwamitin majalisar wakilan Amurkan ranar Laraba cewa hafsoshin sojan rundunarsa sun kai ziyarce-ziyarce zuwa wadannan kasashen biyu ya kuma ce lokaci ya yi na fara cikakkiyar tattaunawa kan wannan batu. ‘’Yanzu mun kai lokacin aiwatarwa don mun wuce maganar yanke shawara.’’ Ya ce. Janar Jones ya ce wannan shawara ta kafa sansanonin sojan Amurka a Romaniya da Bulgeriya na cikin shirin ma’aikatar tsaro na sake tsara zaman dakarun Amurka a fadin duniya. Tsarin ya ce shine na janye dakaru daga sansanoni manya dake kusa da wuraren da ake rikici zuwa kananan sansanoni inda za a yi amfani da su. ‘’Muna farin ciki game da wannan kokari a Turai na kafa rundunar soja wadda za a rinka matsarwa daga Romaniya zuwa Bulgeriya tare da kayan aikin dakarun sama da kuma sauran kayan aikin da ake bukata.’’ Ya kara da cewa. Runduna daya ta kunshi sojoji dubu uku zuwa dubu biyar tare da bangarorin da za su taimaka musu.

Janar Jones wanda shine babban kwamandan dakarun NATO ya ce tattaunawar da sababbin mambobin kungiyar NATO kan samar da wannan sansanoni zata kankama ne kwanannan kuma za ta hada da batun tasoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama da kuma kayan aikin sojan kasa. Ya ce, ‘’na yi imani cewa za mu samu nasara kan wannan tattaunawa a cikin wannan shekarar, babban burinmu shine mu zama muna da sojanmu a inda yake da kusanci. Kuma sakataren tsaro ya fada ba ma son sojanmu su zama a inda ba za mu iya samunsu cikin sauki ba.’’ A baya dai wasu kasashen da Amurka ta kafa sansanonin sojanta sun hana tura wadannan sojoji kai tsaye zuwa wuraren da ake rikici ko kuma amfani da sansanonin wajen kai hare-haren da basu amince da su ba.

Wannan ya zama matsala ga dakarun Amurka a Turkiya a lokacin da aka fara yakin Iraqi shekaru biyu da suka wuce. Amma Janar Jones ya ce ba ya tsammanin faruwar irin wannan matsala da Rumaniya da kuma Bulgeriya wadanda ya ce suna da karamci matuka kum suna sha’awar ganin bangaren babbar rundunar Amurka a Turai a cikin kasashensu. Sai dai Janar din bai tabo maganar kisan da dakarun Amurka suka yiwa wani sojan Bulgeriya ba bisa kuskure a makon da ya wuce.

XS
SM
MD
LG