Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rice ta yabawa Mexico kan harkar tsaro - 2005-03-14


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Madam Condoleezza Rice ta kai ziyarar kwana daya zuwa Mexico a jiya Alhamis. Wannan ziyara ana ganinta a wani matakin share hanyar ziyarar shugaba Vicente Fox zuwa gonar iyalan shugaba Bush ta Crawford a ranar ashirin da uku ga wannan watan.

Sakatariyar ta ce ziyarar zuwa Mexico ta samar da wata dama ta tattaunawa kan batutuwa da dama har da harkar tsaron kan iyaka da harkar kula da shigi da fici. A jawabinta a ma’aikatar harkokin wajen kasar Rice ta ce ta lura da mahimmancin aikin kula da shigi da fici da kuma irin siyasar da ke cikinsa. Mexico dai na bukatar wani shirin bayar da izinin zama na wucin gadi ga miliyoyin ‘yan kasarta da ke cikin Amurka kuma tuni shugaba Bush ya tura doka kan wannan batu zuwa majalisar dokokin kasar.

Sakataritya Rice ta ce batun shigi da fici na daya daga cikin mahinman abubuwa da ta tattauna da shugaba Fox na Mexico a fadar gwamnata ta Los Pinos. Madam Rice ta yabawa Mexico saboda hadin kan da ta ke bayarwa kan yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kuma jaddada mahinmancin kara tsaurara tsaro a kan iyakoki don magance hare-haren ta’addanci. Da ta ke magana kan wani shiri mai suna Minute Man a kudu maso yamma na jihar Arizon wanda ya samar da ‘yan sa kai masu lura da shigowar bakin haure Rice ta ce fadar gwamnatin Washington ba ta yarda da masu aikin sa idon da basa bisa doka ba.

Ta ce, ‘’ a zahiri gwamnatin Amurka ba za ta yarda da wani shirin sa idon da baya bisa doka ba don hana shigowa cikin kasa ba bisa ka’ida ba. Wannan batu zai samu kulawar jami’an kula da shigi da fici kuma muna aiki tare da abokan aikinmu na Mexico don ganin cewa kan iyakokinmu sun samu cikakken tsaro kuma yana da mahinmanci a girmama dokokin Amurka.’’

XS
SM
MD
LG