Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dokokin Iraqi ta fara zamanta - 2005-03-16


Zababbiyar majalisar dokokin kasar Iraqi ta farko a tarihin kasar tun kusan shekaru hamsin ta fara zamanta na farko a dai-dai lokacin da tattaunawa kan kafa gwamnati ke ci gaba. Majalisar da ta kunshi mambobi dari biyu da saba’in da biyar ta fara zamanta cike da matakan tsaro a zauren taronta dake yanki mai cike da tsaro na Green Zone na birnin Bagadaza.

Sai dai awanni kafin bude zaman majalisar an samu fashe-fashe a yankin. Amma ba a san abinda ya haddasa fashe-fashen ba da kuma yawan wadanda suka halaka ko kuma raunata. Ana dai ci gaba da tattaunawa tsakanin mabiya Shian Iraqi da kuma Kurdawa a kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Ita da gamayyar jam’iyyun mabiya Shia sun samu dan karamin rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar. Sai dai tana bukatar samun goyon bayan Kurdawa don samun rinjayen kashi biyu cikin uku don zabar majalisar shugaban kasa wadda za ta fitar da firaminista. A Baquba dake arewacin Bagadaza mota mai dauke da bam ta yi bindiga a yau Laraba a wani wurin duba motoci kuma akalla sojojin Iraqi uku sun halaka.

XS
SM
MD
LG