Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rice da Koriya ta Kudu sun kalubalanci Koriya ta Arewa kan tattaunawar nukiliya - 2005-03-21


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Madam Condoleezza Rice da takwaranta na kasar Koriya ta Kudu Ban Ki-moon a ranar Lahadi sun nemi da Koriya ta Arewa da ta dauki matakin da ya dace na dawowa da tattaunawar kasashe shida kan batun makamanta na nukiliya.

Madam Rice ta ce ita da ministan harkokin wajen Koriya ta Kudun sun amince da kara kaimi wajen ganin an kawo karshen batun makaman nukiliyar Koriya ta Arewa ta hanyar lumana da diflomasiyya. Ta ce, ‘’mun kuma amince da cewa tattaunawar kasashe shidan ita ce hanyar da ta fi, abinda zai sa Koriya ta Arewa ta samu girmawawa da taimakon da ya dace.’’ Koriya ta Arewa dai ta janye daga wannan tattaunawar kasashe shida ne a watan jiya. Kasashe shidan sune Amurka da Koriya ta Kudu da Rasha da China da kuma Japan. Koriya ta Arewan ta ce saboda irin ji-ji da kan Amurka za ta ci gaba da kera makaman nukiliya don kare kanta.

Kafin ta dawo cikin tattaunawar Koriya ta Arewan ta ce tana bukatar neman afuwan Madam Rice kan yadda ta bayyana kasar da ta yi da wani shingen danniya a makwannin da suka wuce. A baya dai ta nemi da ta samu gagarumin taimako daga Amurka da kuma tattaunawa ta kai tsaye da kuma wani tabbaci kan tsaronta. Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu Ban Ki-moon ya ce za a duba dukkanin damuwar Koriya ta Arewa akan tebirin tattaunawar, ya kuma ce wannan tattaunawar ta kasashe shida za ta bayar da damar tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Sakatariya Rice ta kuma amince cewa za a iya samun tattaunawa ta dai-dai da dai-dai da Koriya ta Arewa a lokacin tattaunawar tsakanin kasashe shidan amma ta ce ba za a samu tattaunawa ta daban ba tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa. ‘’Idan muna kan tebirin tattaunawar za mu iya magana da kowa amma a cikin tattaunawar kasashe shidan, ‘’ ta ce. Amurka dai ta dage cewa duk wata tattaunawa dole ta hada da manyan kasashen Asiya. Rice ta kuma nanata matsayin Amurka na cewa bata da niyyar kai hari kan Koriya ta Arewa. Ta ce tattaunawa tsakanin kasashe shidan ne zata tabbatar da tsaro ga Koriya ta Arewa da kuma ceto tattalin arzikinta.

Koriya ta Kudu ta halarci tattaunawa sau uku a Beijing tun daga lokacin da Amurka ta soki kasar ‘yan kwaminis din da kokarin mallakar makaman nukiliya ba bisa ka’ida ba a shekara ta dubu biyu da biyu abinda ya saba dokokin kasashen duniya. Sai dai babu wata nasara kan wannan batu na dakatar da shirin, hasali ma Koriya ta Arewa ta yi ikirarin mallakar bama-bamai masu yawa.

XS
SM
MD
LG