Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dokin Iraqi na shirin kafa sabuwar gwamnati - 2005-03-23


‘Yan siyasar Iraqi sun ce masu tattaunawa daga bangaren Shia da Kurdawa sun kammala tattaunawar kafa gwamnatin kawance kuma ana sa ran majalisar za ta zauna a wannan makon don zabar kakinta. ‘Yan siyasar sun ce da alama ‘yan mabiya Shia za su rike ma’aikatu goma sha shida zuwa sha bakwai su kuma Kurdawa su rike ma’aikatu takwas wadanda za su hada da ma’aikatun mai da harkokin kasashen waje. Sun kuma ce mabiya Sunna wadanda basu da rinjaye wadanda kuma yawanci suka kauracewa zaben a watan Janairu kila su samu ma’aikatu hudu zuwa shida.

Yan mabiya Shia da Kurdawa wadanda ke da rinjayen kashi biyu cikin uku a cikin majalisar dokokin mai mambobi dari biyu da saba’in da biyar na tattaunawar kafa gwamnati tun makwannin da suka wuce. A wani batu kuma sarki Abdullah na Jordan ya umarci jakadan kasarsa a Iraqi da ya koma Iraqin a wani kokarin kawo karshen matsalar diflomasiyya.

An dai fara samun wannan matsalar diflomasiyya ne bayan da wasu ‘yan Iraqi masu zanga-zanga kan rahotan hannun wani dan kasar Jordan a wani harin kunar bakin wake a watan jiya suka daga tutar kasar Iraqin a ofishin jakadancin kasar Jordan. A ranar Lahadi kasashen biyu sun kirawo jakadunsu gida.

XS
SM
MD
LG