Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban ‘yan hamayyar Zimbabwe ya yi alkawarin sauye-sauye - 2005-03-28


A Zimbabwe, jam’iyyun siyasa na kammala yakin neman zaben 'yan majalisar kasa na ranar Alhamis. Magoya bayan jami’yyayar hamayya ta Movement for Democratic Change (MDC) wadanda aka kiyasta sun kai dubu talatin ne suka halarci taron na jiya Lahadi.

Shugaban MDC Mista Morgan Tsvangirai ya nemi mutanen Zimbabwe da su zabi jam’iyyarsa don kawo karshen mulkin zaluncin shekaru ashirin da biyar na Robert Mugabe na jam’iyyar ZANU-PF. Mista Tsvangirai ya ce kodayake shugaba Mugabe ya taka rawa wajen samun ‘yancin Zimbabwe daga hannun ‘yan mulkin mallaka kimarsa yanzu ta zube.

Ya ce, ‘’ idan ka duba irin shugabancin Mugabe cikin shekaru biyar da suka wuce za ka ga akwai matukar gazawa. Ta yaya zaka hana mutanenka abinci? Ta yaya zaka tursasa mutanenka? Ta yaya zaka dauki wani matakin kamfen na tashin hankali kan mutanenka? Yanzu abinda muke bukata shine sabon yanayi da sabuwar Zimbabwe wadda za ta iya magance matsalolin da muke fama da su.’’ Mista Tsvangirai ya kuma ce idan jam’iyyarsa ta samu rinjayen da ake bukata a zaben da za a yi za ta soke dokokin da gwamnatin Mugabe ta kirkiro wadanda ya ce sun danne hakkin ‘yan kasar. Ya kuma sha alwashin farfado da harkar lafiyar da ta durkushe da tabbatar da cewa duk yaran kasar sun samu ilimin firamare kyauta, tsofaffi kuma sun samu kulawar da ta dace. Ya kuma yi alkawarin neman taimakon kasashen waje don shawo kan matsalar rashin abinci da ake fama da shi a kasar. Jam’iyyar MDC zata shiga wannan zaben ranar Alhamis tare da korafin cewa tsarin zaben ya fi bayar da dama ga jam’iyya mai mulki ta ZANU-PF.

XS
SM
MD
LG