Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China ta tura tawaga zuwa Koriya ta Arewa - 2005-03-29


Kasar Sin ta tura abinda ta kira wata tawagar fata zuwa Koriya ta Arewa a kokarin jawo hanakalinta na komawa tattaunawa da sauran kasashe shida kan batun makaman nukiliyarta. Wannan tattaunawa ta zo a lokacin da mai sa ido kan tattaunawar na Amurka ya ke tababar shirin komawar Koriyar kan tebirin tattaunwar.

Tawagar ta Sin na karkashin Ma Wen wani babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar kuma ta baro Beijing ne yau Talata don yin jerin tattaunawa da jami’an Koriya ta Arewa.Masu nazarin al’amuran yau da kullum na hasashen cewa bangaren jami’an kasar Sin din zasu bada karfi kan batun ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyar Koriyan tsakanin kasashe shida, tattaunawar da Koriyan ta kauracewa tun bara.

A wata hira da ‘yan jaridu mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Liu Jianchao ya kira wannan ziyara da irin wadda aka saba tsakanin kasashen biyu amma ya ki yin karin bayani kan batutuwan da za a tattauna lokacin ziyarar. Amma kuma ya ce zai bayar da bayani ne kawai bayan tattaunawar. Wannan ziyara ta zo ne bayan da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice a makon jiya ta kai ziyara Beijing ta kuma nemi da kasar Sin ta kara sa matsi kan Koriyan domin ta koma kan tebirin tattaunawar kasashe shida kan batun makamanta na nukiliya. Kasar Sin dai ita ce babbar mai samarwa da Koriyan abinci da makamashi.

Shi ma firaministan Koriyan ta Kudu ya kai ziyara Beijing a makon jiya a inda ya ce gwamnatinsa ba wai ba za ta koma kan tebirin tattaunawar bane amma dai ba ta sa rana ba. Kuma ita dai Koriyan na neman gafara daga wurin sakatariyar harkokinn wajen Amurka saboda ta bayyana Koriya da wani yankin danniya. Da ya ke magana bayan ganawa da shugabar Philippine Gloria Arroyo, babban mai wakiltar Amurka a tattaunwar ya yi tababar amincewar Koriya na komawa kan tebirin sulhun. Kasashen da ke tattaunawar sune Japan da Amurka da Rasha da Koriya ta Arewa da ta Kudu.

XS
SM
MD
LG