Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban  majalisar dattijan Nigeria, ya sauka daga karagar mulkin sa - 2005-04-05


Shugaban majalisar dattijan Nigeria, ya sauka daga karagar mulkin sa, shine na uku daga cikin manyan ƙusoshin gwamantin kasar da aka tilastawa sauka daga mukamansu a sakamakon matakan da gwamnatin kasar ke dauka na yaƙi da cin hanci.

Mr Adolphus Wabara ya mika takardunsa na yin murabus a yau Talata da safe kafin lokacin da ’yan majalisar su fara wata ganawa. Shugaban majalisar dattijan shine mutumi na uku a jerin masu rike da manyan mukamai bayan shugaban ƙasa da mataimakinsa. Wajejen karshen watan jiya na Maris ne shugaba obasanjo ya zargi shugaban majalisar da laifin karbar cin hanci daga ministan Ilmin kasar Fabian Osuji wanda tunin shugaban kasar ya koreshi.

An zargi tsohon ministan ilmin ne da laifin baiwa shugaban majalisa da kuma wasu ’yan majalisar cin hanci domin su amince da kasafin kudin ma’aikatarsa da ya gabatar wanda ciki ya kara farashin komai domin ya sami moro-moro daga karshe. Jiya litinin kuma, shugaban kasar ya kori ministansa mai kula da gidaje Alice Monbolaji Osomo bayand a tayi watsi da bukatar da aka gabatar mata akan ta soke wani cinikin gidajen jama’a da aka sayarwa manyan ma’aikatan gwmnatin kasar. Jiya Litinin ɗin ne aka gabatar da tsohon sfetan ’yan sanda, Tara Balogun da laifin sata da kuma tara kudin haram wajen dala miliyon 100. Muna da karin bayani bayan labaru

XS
SM
MD
LG