Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon shugaban Iraqi, Jalal Talabani, ya ce yana fata Kasarsa zata iya shiryawa... - 2005-04-11


Sabon shugaban Iraqi, Jalal Talabani, ya ce yana fata Kasarsa zata iya shiryawa domin janye sojojin Amurka da na taron dangi a cikin shekara biyu. Mr. Talabani, ya shaidawa gidan telebijin na CNN cewa akwai bukatar ci gaba da zaman sojojin kasdasahen waje a Iraqi har sai kasar ta sake gina rundunar sojojinta, abinda yake ganin zai dauki shekaru biyu.

A cikin ’yan kwanakin nan, ’yan mazhabin Shi’a sun yi zanga-zangar neman a janye sojojin Amurka ba tare da jinkiri ba daga kasar. A halin da ake ciki, ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce wata kungiyar ’yan ta-kifen da ba a san da zamanta ba a da, ta sace wani ma’aikacin ofishin jakadancin Pakistan dake Bagadaza.

Haka kuma, babu wani sabon labari da aka ji dangane da wasu Romaniyawa ’yan jarida su uku tare da tafintarsu dan Iraqi da aka sace makonni biyu da suka shige a kusa da Bagadaza. Har ila yau, babu wanda ya san abinda ya samu wani janar dan kasar Iraqi da aka sace a makon da ya shige.

XS
SM
MD
LG