Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan sandan kasar haiti sun kashe wani sanannen madugun ’yan tawaye... - 2005-04-11


Yan sandan kasar haiti sun kashe wani sanannen madugun ’yan tawaye da ake nema ruwa ya jallo dangane da kashe wasu ’yan sanda hudu a farkon shekarar nan. Jami’ai sun fada jiya lahadi cewar an kashe Jean Rene Anthony a musayar wuta da ’yan sanda kusa da Port-au-Prince, babban birnin kasar.

An yi wannan musayar wuta kwana guda a bayan da hukumomin haiti suka kashe wani madugun ’yan tawayen mai suna Remissaninthe Ravix, a wani dauki-babu-dakin. Mr. Ravix, wanda ya ayyana kansa a zaman shugaban rundunar sojojin kasar Haiti da aka rushe, yana daya daga cikin shugabanni hudu na tawayen da aka tayar a watan Fabrairun 2004 wanda ya tilastawa shugaba Jean Bertrand Aristide na lokacin ya gudu ya bar kasar. Jami’an Haiti sun yi ta neman mutanen biyu cikin ’yan makonnin nan dangane da karkashe ’yan sanda da aka yi.

XS
SM
MD
LG