Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau ana zaman dar-dar da rashin kwanciyar hankali a birnin Kudus - 2005-04-11


Yau ana zaman dar-dar da rashin kwanciyar hankali a birnin Kudus inda dubban dubatan Yahudawa suka shirya gudanarda wata gagarumar zanga-zanga kuma a cikin wuraren ibadar karimtawa na Musulmi da bani Yahudu din. Masu wannan gangamin suna son bayyana rashin amincewarsu ne da shirin da Isra’ila ke yi na fitarda sojanta daga Zirin Gaza.

Shi dai birnin Kudus a cikinsa Masallacin Al-Aqsa da Musulmi ke darajantawa yake, kuma Palesdinawa sun lasa takobin tada zaune tsaye idan wadannan Yahudawan suka kuskura suka shiga masallacin. Ba ma abinda ya kara cakuda wannan halin zaman dar-dar din kamar kisan gillar da sojan Isra’ila suka yiwa wasu matasan palesdinawa su ukku jiya, har suka kashe su.

Sojan Isra’ila din dai sun nace da cewa sunga wadannan matasan suna rarrafe ne a cikin wani kebantaccen yankin da ba’a barin a shiga, har ma sukace sun hango yaran sun ruga, sun tasarwa Isra’ila, kuma sunki tsayawa duk da harbi cikin iskan da aka yi na yi musu jan kunne. To amma Palesdinawa sunce ba haka abin yake ba, matasan suna wasansu na kwallon kafa ne lokacinda aka harbe su har Lahira. Shi kansa shugaban palesdinawa, Mahmud Abbas yace wannan kisan ya karya yarjejeniyar sulhun da suka kulla da Isra’ila a watan Febrairun da ya gabata.

XS
SM
MD
LG