Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A yau laraba za’a budema jama’a kushewar Papa Roma John Paul na biyu - 2005-04-13


A yau laraba za’a budema jama’a kushewar Papa Roma John Paul na biyu, kwanaki biyar bayan an yi jana’izar shi.

Mabiya za su samu damar ziyartar kabarin da ke cikin babbar majami’ar Saint Peter, wanda aka lullube da farin dutsin da ake kira marble ko marbre, sannan akan kabarin, aka rubuta sunan shi da shekarun da ya yi, ya na rike da mukamin Papa Roma.

A jiya talata manyan jami’an Majami’ar Roman Katolika da ake kira Cardinals su ka ziyarci kabarin, har su ka yi addu‘a.

Ranar litinin mai zuwa za su fara zaman su na sirri domin zaben wanda zai maye gurbin Papa Roma.

A wani al’amari na daban kuma, fadar Vatican ta ce a ƙalla maziyarta miliyan ukku ne su ka je birnin Roma bayan mutuwar Papa Roma a ranar 2 ga watan afrilu, wato a kowace sa’a ɗaya an samu kwatankwacin mutane dubu 21 da su ka tsaya a kan gawar shi.

XS
SM
MD
LG