Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Thabo Mbeki na ATK, wanda yake shiga tsakani a kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar Ivory Coast - 2005-04-14


Shugaba Thabo Mbeki na ATK, wanda yake shiga tsakani a kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar Ivory Coast, ya bayar da shawarar cewa a kyale kowa ya tsaya takarar shugaban kasa, matakin da yana daya daga cikin muhimman bukatun ’yan tawayen arewacin kasar.

Jami’ai daga sassan kasar masu yadar juna sun shaidawa Muryar Amurka cewa wannan shawara tana kunshe a cikin wasikar da shugaban an ATK ya aikewa da gwamnatin Ivory Coast, da ’yan tawaye da kuma jam’iyyun hamayya.

Sharrudan cancantar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa suna daga cikin manyan batutuwan da ake takaddama a kai a yakin basasar da ya raba kasar gida biyu tun 2002. ’Yan tawayen dake rike da bangaren arewacin kasar suna son a kyale shugaban ’yan hamayya Alassane Ouattara ya tsaya takarar shugaban kasa, yayin da gwamnati take fadin cewa bai cika ka’idojin da aka shimfida cikin tsarin mulki na tsayawa takarar wannan kujera ba.

XS
SM
MD
LG