Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata gobarar da ta tashi a wani hotel a tsakiyar Paris... - 2005-04-15


Wata gobarar da ta tashi a wani hotel a tsakiyar Paris babban birnin kasar Faranshi ta halaka mutane 12 a kalla, wasu kuma 55 sun jikkata, wasun su, su yi munanan raunuka.

‘Yan sandan kasar Faranshi sun ce da jijjifin yau Juma’a gobarar ta tashi, a lokacin da baki ke shara barci a hawa na shidda a otel Paris-Opera. Jami’ai sun ce wasu bakin hotel din sun dira ta tagogi domin su tsira daga gobarar.

Motocin kashe gobara fiye da 50 da motocin daukan marasa lafiya 10 aka kira wurin da ke kusa da ginin Garnier mai tarihi a birnin inda ake wasan opera, babban abun da ke jan ’yan yawon shakatawa da bude ido.

Har yanzu hukumomin kasar Faranshi ba su tantance musababbin gobarar ba.

XS
SM
MD
LG