Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hafsoshin sojan Turkiyya sunce an gwabza fada tsakanin sojan nasu da mayakan kungiyoyin ‘yantawayen Kurdawan - 2005-04-15


Hafsoshin sojan Turkiyya sunce an gwabza fada tsakanin sojan nasu da mayakan kungiyoyin ‘yantawayen Kurdawan Turkiyya a gabashin kasar inda har su sojan suka kashe dakaru 10 na ‘yantawayen.

Wasu rahottani ma sunce yawan wadanda aka kashen sun kai 21, kuma dukkansu mayakan jam’iyar Kurdawa ta P-K-K ne. Sai dai suma sojan Turkiyya din an kashe nasu sojojin guda ukku a cikin wannan fadan da ya gwabce a a wani yanki dake tsakanin lardin Siirt da lardin Sirnak.

Tun cikin watan Yunin bara fadan ya kincime a wadannan yankunan na kudu-maso-gabashin Turkiyya bayanda su ‘yantawayen suka ce sun tsinke yarjejeniyarsu ta sulhu da gwamnati bayanda suka zargi gwamnatin da cewa ba “ta rama wa kura anniyarta” wajen neman sulhunta al’amurra kamar yadda su, suke yi.

Su dai wadannan ‘yantawayen Kurdawan tun 1984 suke yakin nemar wa kansu ‘yantaccen yanki, kuma, daga lokacin zuwa yanzu, an hallaka mutane sun fi dubu 30, galibinsu duk Kurdawa.

XS
SM
MD
LG