Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani yunkuri da gwamnatin kasar Chad tayi na daukaka darajhar mata - 2005-04-18


Wani yunkuri da gwamnatin kasar Chad tayi na daukaka darajhar mata, kare hakkinsu da karfafa ‘yancinsu ya abka cikin adawa daga jagabannin Musulmi da na Kiristocin kasar duk baki dayansu.

Hakan ta faru ne bayanda shugaba Idriss Deby na kasar ya bayyana amincewarsa ga wata dokar iyali da ake son a kafa wacce ke son kawarda yawan banbance-banbacen dake tsakanin maza da mata – da kuma hanawa maza dukan matansu, har ma da neman kara yawan albashin da ake biyan mata in suna aiki.

To amma shehunan malaman Musulunci sunce wannan matakin da gwamnatin ke son dauka ya sabawa ka’idojin addinin na Islama, yahyinda jagabannin kiristoci kuma suka ce su sam ba zasu taba yarda da wasu sassa na dokar dake karfafa da kuma hallata auren mata da yawa ba.

Wannan dokar tafi shekaru ukku tana zaune a hannun gwamnati, an rasa yadda za’a yi da ita, musamman da yake ance wasu ministoci da gangan suke kin barin a tado da zance akanta – don basa son a kai ga kafa ta!

XS
SM
MD
LG