Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani babban jami’in Masar ya ce kasarsa tana shirin ninka yawan sojojinta dake cikin rundunar KTKA a yankin Darfur - 2005-04-21


Wani babban jami’in Masar ya ce kasarsa tana shirin ninka yawan sojojinta dake cikin rundunar KTKA a yankin Darfur mai fama da fitina a kasar Sudan. Ministan harkokin wajen Masar, Ahmed Aboul Gheit, ya ce shugaba Hosni Mubarak ne yayi wannan alkawari a lokacin taron kolin da yayi ranar talata da shugabannin Sudan, Ethiopia da Nijeriya a wurin shakatawar Sharm el-Sheikh dake gabar bahar Maliya.

Mr. Gheit ya ce shugaban KTKA mai ci, shugaba Oluegun Obasanjo na Nijeriya, ya kuduri aniyar karfafawa kasashen Afirka guiwar su kara yawan mutanensu a darfur. A yanzu haka dai, masar tana da sojoji 100 a cikin sojoji fiye da dubu 2 na KTKA dake darfur. Mutane fiye da dubu 200 sun hallaka a cikin shekaru biyun da aka yi ana bai wa hammata iska a tsakanin ’yan tawaye da ’yan banga ’yan barandan gwamnatin Sudan a yankin na Darfur, yayin da wasu mutanen su kusan miliyan 2 ala tilas sun gudu sun bar gidajensu.

XS
SM
MD
LG