Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan tawaye da askarawan gwamnati a kasar Cote d’Ivoire sun fara janye manyan makaman su - 2005-04-22


‘Yan tawaye da askarawan gwamnati a kasar Cote d’Ivoire sun fara janye manyan makaman su daga fagagen daga, domin aiwatar da wata sabuwar yarjejeniyar da aka kulla a kasar da ke rabe gida biyu.

Ana kyautata zato, kwanaki hudu za su yi su na kwashe makaman da su ka fara yi a jiya alhamis. Makaman da za’a kwashe sun hada da manyan bindigogi da makaman igua masu cin gajeren zango. Makaman yaƙi da tankoki kawai za’a bari a girke a fagagen dagar.

Sojojin kasar Faranshi dubu 4 da jami’an MDD masu tsaron zaman lafiya sama da dubu shiddan da aka tule a kasar ta Cote D’Ivoire, su ne za su kula da matakin kwashe makaman yakin.

Manzo MDD a kasar Cote d’Ivoire, Pierre Schori, ya bayyana matakin a zama mai bada kwarin guiwa.

Yarjejeniyoyin sulhun farko-farkon da aka yi ta kullawa a kasar ta Cote d’Ivoire, sun kasa bada biyan bukata. Tun bayan wani boren da sojoji su ka yi a watan satumban shekarar dubu biyu da biyu, rabin arewacin kasar ya fada hannun ’yan tawaye.

XS
SM
MD
LG