Shugaban rikon kwarya na kasar Togo, Abbas Bonfoh yace ba makawa, zaben shugaban kasan da aka shirya yi gobe Lahadi, za’ayi shi. Jiya ne Mr. Bonfoh yake bada wannan tabbacin, kwana daya bayanda ya kori ministan harakokin ciki gida na kasar, Francois Boko saboda katobarar da yayi na cewa kila zaben ba zaimyiwu ba saboda tsoron barkewar tashin hankali. Ministan ya furta cewa, saboda tsoron barkewar tashin-tashinar, mai yiyuwa ne adage zaben, a bar shi sai bayan shekara daya ko biyu ayi shi.
Suma ‘yan adawar Togo sun nemi a jinkirta zaben, har suka zargi gwamnati da cewa ta shirya babban magudi. Jiya ma dubban mutane sunyi zanga-zanga a Lome, babban birnin kasar, wasunsu dauke da adduna da kulake.
Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma ne dai suka matsawa Togo sai ta shirya wannan zaben, bayan mutuwar ba-zata da tsohon shugabanta Gnassingbe Eyadema yayi a cikin watan Febrairun da ya gabata.