Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zacarias Moussaoui, mutumen da har zuwa yanzu shi kadai ne aka gurfanar a gaban kuliya bisa zargin taka rawa a harin 11 ga watan Satumban 2001 - 2005-04-24


Zacarias Moussaoui, mutumen da har zuwa yanzu shi kadai ne aka gurfanar a gaban kuliya bisa zargin taka rawa a harin 11 ga watan Satumban 2001 da aka kawo Amurka, ya amsa laifin kulla makarkashiyar kawo farmakin. A jiya ne M. Moussaoui ya amsa wannan laifin sadda ya bayyana a gaban wata kotun tarayyar Amurka dake a jihar Virginia, inda aka dada jaddada zargin da ake masa na cewa ya hada kai da kungiyar Al Qaida wajen kawo wannan harin na 9/11.

Zargin ya ambaci cewa ana tuhumarsa da laifin hada baki da wasu wajen kai harin ta’addanci, nakassa jiragen sama da kuma hallaka ma’aikatan gwamnati. Shi da bakinsa M. Moussaoui ya gayawa kotun cewa, koda yake shi kansa baya cikin wadanda suka kawo harin, yana cikin wani bangare na wadanda suka shata makarkashiyar anfani da jirgin sama wajen rabka jirgin akan fadar White House ta shugaban Amurka.

Atone-janar na Amurka Alberto Gonzales ya ce Moussaoui ya shatawa hukumomi karya bayanda aka cafke shi a watan Agustan 2001, wanda wannan karyar tasa ce ma ta baiwa su sauran ‘yan Al-Qaida damar kawo harin. Mr. Gonzalez yace zasu nemi a yanke hukuncin kisa akan M. Moussaoui.

XS
SM
MD
LG