Hukumar zaben kasar Togo to fidda sakamakon zaben ran lahadiinda tace Faure Gnassimgbe ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar. Anji shugaban hukumar zaben ta kasar Togo Kissem Tchangai-Walta na cewa Gnassimbe, dan tsohon shugaba Eyedema, ya sami kashi sittin daga cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.
Mintoci kadan da bayyana wannan sakamako, sai matasan jam’iyyun hamayya suka fantsama kan titunan birnin Lome suna zanga-zanga da cinna wuta tare da jifa da duwatsu a kan motoci. Daman tun shekaranjiya lahadi aka fara tunzuri saboda zargin yin magudi a rumfunan zaben da shugabannin kungiyar ECOWAS suka tilasta yi bayan da soja suka mika ragamar mulki hannun Faure Gnassimgbe a watan Fabarairu.
Hukumar zaben kasar Togon tace dan takarar hamayya Akitani-Bob ya sami kashi talatin da takwas daga cikin dari na yawan kuri’un da aka laɗa, sannan dan takara na uku Harry Olympio yazo na karshe da kasa da kashi daya daga cikin dari.