Jami‘an rundunar sojin Amurka a Iraqi sun ce jagoran ’yan gwagwarmaya Abu Musab al-Zarqawi da suke nema, wanda ya kaucewa tarkon kama shi da alamar ya bar Iraqi, amma ya bar wasu muhimman sahihan bayanan ayyukan leken asiri da za‘a yi amfani dasu.
Rundunar musamman da aka dankawa aikin lallai su kamo shi, ta bayyana cewa anga Zarqawi ya daka tsalle daga wata motar da yakeciki a kusa da inda soja ke bincike ya gudu a ran 20 ga watan fabarairun da ya gabata a kusa da birnin Ramadi dake Yammaci. Sojin Amurka sun bi motar da ya fita daga cikinta har zuwa inda ta tsaya, sannan suka binciki motar suka tadda injin komputa mallakar Zarqawi da kuma kudi Dola dubu dari da kuma takardun kudi na Euro.
Amma sun sami nasarar kama daya daga cikin abokansa yanzu haka yana tsare. Yanzu dai Abu Musab al-Zarqawi ne a sahun gaban wanda Sojin Amurka ke nema a Iraqi. Amurka tayi alkawarin bada ladan Dola miliyan ashirin da biyar ga duk wanda ya taimaka aka kama shi.