Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga a Iraq sun kashe wata ‘yar majalisar kasar a yau laraba. - 2005-04-27


‘Yan bindiga a Iraq sun kashe wata ‘yar majalisar kasar a yau laraba. Wannan mace ita ce ta farkon da aka kashe daga cikin ‘yan majalisar rikon da aka zaba cikin watan Janairun da ya gabata. ‘Yan sanda suka ce ‘yan bindigar sun harbeta ne a kofar gidan na birnin Bagadaza.

A halin da ake ciki ‘yan shi’a daga cikin jami’an gwamnati sun ce an sake jinkirta shirin kafa sabuwar gwamnati, saboda ‘yan siyasar kasar sun kalubalanci wasu daga cikin sunayen da Fira Minista Ibrahim Ja’afari ya gabatar domin su zama ministocin sabuwar gwamnatin.

Amm dai kwamitin da shugaban kasar ya kafa mai mai mambobi uku ya amince da dukkanin sunayen minstocin, kafin ita kuma majalisar kasar mai mambobi metan-da-saba’in-da-biyar ta kada tata kuri’ar-amincewar. A wata daban kuma, gwamnatin Romeniya ta roki wadanda suka sace ‘yan jaridar kasarta uku a Iraqin, da su kara mata lokaci.

A yau Laraba ce, ‘yan-satar-mutanen suka yi barazanar zasu kashe su, sai dai idan kasar Romeniyan ta janye dakarunta daga Iraq.

XS
SM
MD
LG