Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan kasa da kasa sun fara wata tattaunawar nazartar yada ake aiki da daftarin yarjejeniyar... - 2005-05-02


Wakilan kasa da kasa sun fara wata tattaunawar nazartar yada ake aiki da daftarin yarjejeniyar hana bazuwar makaman nukiliya a duniya. Ana wannan zaman tattaunawr ne a birnin New York, matsalar neman kera makaman nukiliyar Korea ta Arewa da Iran ce ta janyo wannan zaman domin sake nazartar aiki da shirin yarjejeniyar.

Amurka na bukatar ganin an sake nazartar kudurin daftarin yarjejeniyar da ake sanyawa hannu a karshen shekaru biyar. Tilawa da sake nazartar daftarin zai taimakawajen gano kasashen dake neman bijirewa dokar bayan sun saka hannu. Wadannan kasashen ko sun hada da Iran da Korea ta arewa.

Amma mafi yawan kasashen da suka sanya hannu a kudurin dokar suna zargin Amirka da sauran manyan kasashe masu karfin arzikin masana’antu wadanda suka riga suka mallakai makaman nukiliya da laifin kin daukan wasu matakan azo a gani da zai nuna suma suna rage rumbunsu na makamai, maimakon hakan sai ci gaba da kera sabbin makamai suke yi.

Domin karfafa wannan zargi da damuwa, babban magatakardar MƊD Kofi Annan yace amincewar da kasa da kasa keyiwa daftarin kudurin ya fara dusashewa. Aka kuma bada misalin cewa ya zuwa yanzu Isra‘ila da Pakistan sun ki sanya hannu a wannan kudurin doka.

Kuma Iran tace ba wanda zai iya hanata ci gaba da aikinta na neman sanadaran kera makaman nukiliya bayan ta amince a baya da ta jingine shirin a wata tattaunawar da Iran din tayi da wakilan kungiyar Tarayyar Turai. Korea ta Arewa ta fice daga gungun kasashen da suka sanya hannu a daftarin yarjejeniyar, kuma ta ayyana cewar ta mallaki makaman nukiliya

XS
SM
MD
LG