Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla mutane 10 suka rasa rayukkansu a sanadin wata kakkarfar fashewar da ta tashi a babban filin wasan Mogadishu - 2005-05-04


Akalla mutane 10 suka rasa rayukkansu a sanadin wata kakkarfar fashewar da ta tashi a babban filin wasan Mogadishu, babban birnin Somalia, a daidai lokacinda frayim-ministan kasar ke jawabi ga taron jama’ar da suka cika filin. Sai dai shi kansa PM Ali Mohammed Gedi ance baiji wani ciyo ba, kuma nan take ma’aikatan tsaro sukayi sauri, suka cacume shi, suka arce da shi.

‘Yansanda dai sunce har yanzu basa da tabbas na abinda ya haddasa wannan fashewar, to amma ministan watsa labaran Somalia, Mohammed Abdullahi Jama ya gayawa V-O-A cewa akwai alamun gurnetin da wani dogari ke dauke da ita ne, ta fadi kuma ta fashe a bisa hatsari irin na kaddara. PM Gedi dai yace wannan al’amari ba zai razana sabuwar gwamnatin wucingadi daga dawowa da zama a cikin kasar ba. A inda aka fiton nan, gwamnatin na zaune tana aiki ne daga Kenya saboda rashin kwanciyar hankali a can Somalia.

A kashin gaskiya ma wannan zuwa da shi PM Gedi yayi shine zuwansa na farko a birnin Mogadishu tun bayanda aka bashi aikin jan ragamar wannan sabuwar gwamnatin, wacce itace ta farko da aka kafa a kasar Somalia a cikin shekaru 13 da suka gabata.

XS
SM
MD
LG