Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an binciken asiri na kasar pakistan sun bayyana kama mutumin da aka yankewa hukuncin kisa - 2005-05-05


Jami’an binciken asiri na kasar pakistan sun bayyana kama mutumin da aka yankewa hukuncin kisa domin samun hannunsa a neman kashe shugaba Pervez Musharaff sau biyu a shekara ta dubu biyu da uku.

Jami’an tsaro sun bayyana yau cewa,an kama Mushtaq Ahmed ne farkon wannan makon a kan hanyarshi zuwa Islamabad daga Lahore.

Wata kotun soji ce ta sami jami’in mayakan saman da wannan laifin ta kuma yanke mashi hukuncin kisa,amma daga baya Ahmed ya tsere daga cibiyar Chakala kusa da sansanin mayakan saman da ke Islamabad inda aka tsareshi.

An yankewa kananan jami’n sojin da dama hukuncin kisa domin samun hannunsu da aka yi a wannan makarkashiyaar.

XS
SM
MD
LG