Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasa A  Botswana


An rantsar da sabon shugaban kasa a Botsuwana.Sabon shugaban kasar shine,Seretse Ian Khama, wanda shine mataimakin shugaban kasan shugaban da ya sauka, ya bayyana cewa zai tabbatarda da dorewar kasa.

Seretse Ian Khama,a jawabinsa a bukin rantsar da shi da aka yi yau, yace sabuwar gwamnatin da aka samu a Botswana bai nuna cewa za a sami wadansu muhimman canje canje a kasar ba.

Magabacinsa, Festus Mogae ya taimaki kasar da ta kasance kasar da tafi kowacce kasa a duniya arzikin duwatsun kawa na Azurfa, ta kasance daya daga cikin kasashen da arzikinsu yake da karfi a nahiyar Afrika. Mr. Mogae ya sauka daga karagar mulki yau, ya kiyaye cikar wa’adin mulkinsa biyu na tsawon shekaru goma.

Sabon shugaban kasar Botsuwanan,wani tsohon kwamandan soji ne wanda ya yi mataimakin shugaban kasar Mr. Mogae. Yace ya shiga aikin soji ne domin kare damokuradiyya, zai kuma ci gaba da goyon bayan wannan tsarin.

XS
SM
MD
LG