Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Da  Aka 'Dana A Gefen Hanya Ya Kashe Akalla Mutane Tara


Mahukumtan Afghanistan sun ce mutane tara sun mutu bayan da bom da aka ɗana a gefen hanya ya tarwatsa ƙaramar motar safa da suke tafiya a ciki.

Yan sanda sun ce bisa ga dukkan alamu anyi fakon dakarun ƙungiyar tsaro ta NATO ne da bom ɗin. Ƙananan yara guda biyu na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a harin na yau. Tun farko a yau ɗin, rundunar sojin Amurka tace an kashe wani soja a kudancin Afghanistan wanda ke aiki ƙarƙashin rundunar haɗin guiwa da Amurka ke jagoranta.

Rundunar sojin Amurka tace sojan ya gamu da ajalinsa ne lokacin da motar da yake ciki ta bi ta kan nakiyar da aka ɗana jiya Litinin. Sojoji da dama dake cikin motar kuma sun jikkata.

XS
SM
MD
LG