Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Taron Dangi A Afhganistan Sun Kashe Sojojin Kasar Tara.


Maaikatar Tsaron Afghansitan tace sojojin kasa da kasa bisa kuskure sun kashe sojojin Afghnaistan tara, suka jikkata wasu uku a farmaki ta sama da suka kai gabashin kasar.

Jami'an Ma'aikatar sunce an kai farmakin ne a wani wurin bincken motoci a dake Khost, a farkon safiyar yau Laraba.Ma'aikatar tayi Allah wadai da harin,tana gargadin cewa irin wannan zai kashe gwiwar Jami'an tsaron Afghansitan.

Sanarwar daga rundunar taron dangi da Amurka takeyiwa jagoranci tace Sojojin suna kan hanyar su daga wani aiki,yayinda fada ya kaure har suka kashe, kuma suka jikkata wasu sojojin Afghanistan. Sanarwar tace wannan matsala ta rashin fahimta ce daga sassan biyu duka.

Kakakin rundunar Amurka Col Greg Julian, yace Jami'an Sojin Afghanistan da na Amurka, zasu gana domin binciken wannan lamari. A kudancin lardin Uruzgan,jami'an Afghanistan sunce sakamakon fada da aka gwabza na kwana biyu tsakanin jami'an tsaro da mayakan sakai na Taliban,an kashe 'yan gwagwarmaya 35,da 'yansandan Afghnaistan uku.

XS
SM
MD
LG