Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alqaida Tana Gargadin Cewa Zata Ci Gaba Da Kai Hari Kan  Muradun Amurka  Idan Amurkan Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Isra'ila


Wani sabon faifan daukan maganar da gidan Telbijin na Al-Jazeera ya baza jiya lahadi, anji shugaban al-Qaida Osama bin Laden na cewa al-qaida ce keda alhakin kokarta tada boma a jirgin saman Amurka da yaci tura a ranar kirsimetin da ta gabata. Anji Osma ben lade na bayyana haka a jiya lahadi.

Osama ben laden yana mai garagadin cewa za’a ci gaba da kaiwa muradun Amurka harin, muddin dai Washington taci gaba da baiwa Isra’ila goyon baya. Bin laden yana mai cewa al-qaida ce ta tura dan Nigeria Umar faruk Abdulmutallab, sannan ya kara jaddada cewar al-qaida ce keda alhakin shirya kai hare-haren sha daya ga Watan Satumba shekarar 2001 har cikin Amurka.

Amma ya zuwa yanzu dai an kasa tabbatar da sahihancin ko muryar dake Magana ta Osama bin laden ce. Kuma Gwamnatin Amurka bata maida martini game da sanarwar ba.

XS
SM
MD
LG