Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Iran Sun Koma Kan Teburin Tattauna Tsaron Iraq


Sa toka sa katsin dake tsakanin Amurka da Iran, kan makomar wadansu Amurkawa ‘yan asalin Iran dake tsare a hannun Iran din a halin yanzu, ba zai zama daya daga cikin batutuwan da za a tattauna a taron na Talata ba.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Sean McCormack yace Jakadan Amurka a Iraq, Ryan Crocker, zai matsantawa Iran ta sauya manufofinta kan Iraq lokacin tattaunawar. Crocker zai tattauna ne da takwaransa na Kasar Iran, Hassan Kazeemi Qoomi.

A watan Mayu wadannan jakadu suka yi zagayen farko na tattaunawa, a mataki mafi girma da kasashen biyu suka taba ganawa tunda suka yanke huldar jakadanci a shekarar 1979. Amurka tayi ta zargin Iran da marawa tsagerun ‘yan Shi’a baya suna tafka ta’asa a Iraq, zargin da Iran ta musanta. McCormack yace baiga wani sauyin hali daga Iran ba tunda aka gudanar da waccan tattaunawa.

A wani labarin kuma, Iran tace yau Talata zata tattauna da jami’an Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Makamashin Atom, a birnin Viennan Austria. Jakadan Iran ga wannan hukuma, Ali Asghar Sultanih ya fada a jiya Litinin cewa tattaunawar da zata duba rikicin yunkurin Iran na mallakar makamin Nukiliya.

Taron, ci gaba ne da wanda aka riga aka gudanar a Tehran a farkon watan nan. Babban mai bincike makamashin nukiliya Olli Heinonen shine ke jagorantar tawagar Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya. Kwamitin Tsaro ya kakaba wa Iran wadansu takunkumai har hawa biyu, saboda kin amincewa da tayi ta dakatar da inganta makamashin uranium.

XS
SM
MD
LG