Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tabbatar Da Ka Hari Kan Kasar Sham (Syria)


Wani kusar gwamnatin Amurka ya tabattarda cewa harin da sojojin Amurka da jiragensu na sama masu saukar ungulu a cikin kasar Sham (Syria), yayi nasarar kashe wani mutum da akace ya jima yana fasa-kwabrin makamai da mayaka zuwa cikin Iraq.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito wannan kusar da ya nemi kada a fadi sunansa kafin yace kala, da cewa ya gaya musu sunan wanda aka kashen shine Abu Ghadiya, wanda tun ba yau ba Baitulmalin Amurka ta bayyana shi da cewa babban mai samarda kuddi ne ga al-Qaida.

Sai dai Syria na zargin Amurka da yi mata “tsokana irin ta ‘yan ta’adda” A sanadin wannan farmakin da tace ya janyo mutuwar mutane takwas.

XS
SM
MD
LG