Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kafa Dokar Hana Yawo Bayan Barkewar Sabon Rikicin Addini A Jos


Shaidun gani da ido sun tabbatar da barkewar sabon rikici a birnin Jos na jihar Plateau jiya lahadi, rahotannin da jami’an Gwamnati basu tabbatar dasu ba na cewa an sami rasuwar mutane masu yawa. Ga dukkan alamu kuma rikicin anyi shine tsakanin Matasan Kirista da na Musulmi.Gwamnatin Plateau ta kafa dokar hana yawon dare daga karfe shida na Magariba zuwa shida na Safiya.Mazauna birnin Jos sun ce an kona gidaje masu yawan gaske.Rundunar ‘yan sanda tace ta kama mutane 35 da ake kyautata cewar suna da hannu wajen tada wutar rikicin. Akwai Karin bayani a rahoton mu na bayan labarai.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da barkewar sabon rikici a birnin Jos na jihar Plateau jiya lahadi, rahotannin da jami’an Gwamnati basu tabbatar dasu ba na cewa an sami rasuwar mutane masu yawa.Ga dukkan alamu kuma rikicin anyi shine tsakanin Matasan Kirista da na Musulmi.Gwamnatin Plateau ta kafa dokar hana yawon dare daga karfe shida na Magariba zuwa shida na Safiya.

Mazauna birnin Jos sun ce an kona gidaje masu yawan gaske.Rundunar ‘yan sanda tace ta kama mutane 35 da ake kyautata cewar suna da hannu wajen tada wutar rikicin.

XS
SM
MD
LG