Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kan Babban Bututun daukar Mai Na Shell A Yankin Niger Delta


Kamfanin mai na Shell a Najeriya ya bada labarin rufe tashoshin 'danyen mai uku a yankin Niger-Delta,sakamakon wani hari da aka kaiwa wani babban butu.

Jami’an kamfanin sunce an rufe tashoshin ne bayan anga mai yana yoyo daga babban bututu dake Ramos. Babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin. Sai dai a ranar Asabar,babbar kungiyar tsagerun yankin Niger Delta, MEND, ta kawo karshen tsagaita wuta tsakaninta da gwmnati,kuma ta lashi takobin ci gaba da kai hare hare kan ma’aikatun mai da ma’aikanatansu.

Kungiyar ta gargadi ma’aikatun mai su kimtsawa hare hare daga kungiyar. MEND tana zargin gwamnatin Najeriya cewa ta lura batadaniyyar mikawa ‘yankin kasarsu da albarkarta,kamaryadda kungiyar ta nema.

XS
SM
MD
LG