Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Yangwagwarmaya Talatin Da Takwas a Iraqi


Rundunar mayakan Amurka a Iraqi tace dakarun ta dana Iraqi sun kashe ‘yan gwagawarmaya 38 a Bagadaza, a wani bata kashin da ta ce shine mafi muni da aka gwabza a cikin ‘yan makonnin nan. Rundunar ta fada litinin din nan, cewa ‘yan bindiga sun fake da guguwar Hamada da ta lullube fadar kasar jiya lahadi wajen kai jerin hare hare. Guguwar ta hana jiragen yaki masu saukar ungulu aiki, wadanda sune manyan makaman da sojojin Amurka suke amfani da su a farautar mayakan sakai masu harba rokoki.

Akasarin fada a jiya a unguwar Sadr akayi, inda nanne tungar mayakan sakai masu biyayya ga shehin ‘yan mashabar shi’a Muqtada al-Sadr. A fada mafi muni mayakan Amurka da na Iraqi sun tilastawa wadanda suka kawo kazamin hari kan wata cibiyar binciken ababan hawa jada baya.

Dakarun Amurka sunce mutum ashirin da biyu cikin mayakan sakai ne aka kashe,ita Amurka da Jami’an Tsaron Iraqi ba a musu hasara ba sam.

XS
SM
MD
LG