A yau Alhamis, hukumomi a Najeriya suka baiyana Kanar Muhammadu Sada Abubakar na uku, a matsayin sabon Sarkin Musulmi, bayan rasuwar yayansa, marigayi Ibrahim Muhammadu Maccido, a hatsarin jirgin saman Lahadin da ta gabata.
Shekarun Sarki Muhammadu Sada Abubakar kimanin hamsin da haihuwa, kuma yana rike da mukamin Jami'in Huldar Tsaro na Najeriya a kasar Pakistan, lokacin da wannan sarauta ta fado masa.
A cikin aikace-aikacen da yayi na soja, har da aiki tabbatar da zaman lafiya a kasar Saliyo.
Kamar Sauran iyaye da kakanninsa, Sarki Muhammadu Sada Abubakar, jikan Shehu Usman Dan Fodiyo ne, mutumin da ya kada daular Musulunci ta Usmaniyya a shekarar 1804. (kimanin shekaru dari biyu da biyu kenan da suka wuce).
Sarki Muhammadu Sada shine Sarkin Musulmi na ashirin, tun daga kan kakansa Shehu Usman Dan Fodio.