Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Sace Mutanen Kasashen Waje  A Neja Deltan Najeriya


Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, tace wadansu ‘yan bindiga sun sace wani ba’amurke daya, da baturen Ingila daya, a kudu maso gabashin kasar. Wani ma’aikacin wani kamfanin man fetur yace an sace mutanen ne a cikin wata motarsu a birnin Fatakwal.

Tsagerun wannan yanki na Niger Delta, sun dade suna kai hare hare kan masna’antun man fetur, a kokarin da suke na samun kaso mafi girma, na arzikin man kasar. A cikin shekara daya kawai, an sace a kalla ma’aikata 60.

A yau din dai, Jami’an kasar Philippines sun bayar da wata sanarwa da tace ‘yan kasarta 24 aka sace a wannan yanki a satin da ya gabata. Rahotannin da aka bayar da farko sun nuna cewa mutum shida aka sace.

Shugaba Gloria Arroyo, ta bayar da umarnin hana ma’aikatanta zuwa Najeriya na wani dan takaitaccen lokaci, har sai an tabbatar da tsaron lafiyarsu.

XS
SM
MD
LG