Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Tsaiko A Zaben Isra'ila


An shiga wani halin rashin tabbas dangane da wanda zai zama Firayin Ministan Isra'ila na gaba, saboda kowa daga cikin manyan jam'iyyun kasar biyu, suna da'awar nasara a babban zaben kasar.

Bayan an kammala kidaya kashi 99 bisa dari na kuri'un da aka kada, Jam'iyya mai mulki ta Kadima, wadda ke karkashin jagorancin Tzipi Livni, ta sha gaban jam'iyyar 'yan mazan jiya ta Benjamin Netanyanhu da kujera daya jal a Majalisa.

Masu sharhi kan al'amuran siyasar kasar sunce ko an kammala kirga ragowar kuri'un, babu daya daga cikin manyan jam'iyyun da zata sami rinjayen da ake bukata, domin kafa gwamnati, gashi kuma Netanyanhu ya ki ya mika wuya, bare ya amince a kafa gwamnatin hadin guiwa.

Sudai masu kada kuri'a sun ce tsaro shine babban al'amarin dake gabansu, abin da yasa suka kada wa 'yan mazan jiya kuri'u masu yawa, kamar yadda Avigdor Liberman, shugaban wata karamar jam'iyya ta Yisrael Beiteinu ya fada.

Liebaerman yace tilas ne a bada fifiko ga yaki da ta'addanci, kuma basu yarda da wata tattaunawa cikin sulhu ba, ko ta kai tsaye, ko ta bayan fage.Liberman yana ma da ra'ayin a ware dukkan 'yan kasar ta Isra'ila masu jinin larabawa, a maida su karkashin mulkin Falsadinawa.

Wani Farfesan kimiyyar siyasa a Jami'ar Hebrew, Abraham Diskin yace mai yiwuwa Netanyanhu ya dare kujerar ta Firayin Minista, duk da cewa yana bayan Livni da kujera daya, saboda kananan jam'iyyu masu ra'ayin mazan jiya sun fi yawan kujeru a majalisar. Saidai yace lallai ne Netanyanhu ya bi sannu wajen zaben wadanda zai kafa gwamnati dasu.

Yace 'Yan mazan jiyan da yake hange, ba lallai su zama masu ra'ayi irin nasa ba, kuma jam'iyyu shida ne masu alkibla bambancin alkibla kan muhimman al'amuran da suka shafi Isra'iala.

XS
SM
MD
LG