Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Jana'izar Sojojin Najeriya Da Aka Kashe A Darfur


An binne sojojin su bakwai a wata makabartar sojoji, dake bayan garin Abuja, babban birnin Najeriya, inda aka lullube akwatunan dake dauke da gawawwakin, da kyallayen tutocin Njeriya da na Kungiyar taraiyar Africa.

Wani mai magana da yawun Rundunar Sojin Najeriya, Kanar Mohammed Yusuf, yace saboda yawan jama’arta, da kuma karfinta na soji, Najeriya tana daukar gabarar tabbatar da zaman lafiya a sauran kasashen Africa.

Shi kuwa Olatunji Toyin, ya je Abuja domin karrama kaninsa Karabiti Ajao Toyin, dan shekaru 25, daya daga cikin sojojin da aka kashe, kuma cikin hawaye, yace suna alfahari da hazakar yaron, da kuma kishin kasarsa. An dai yiwa sojojin bakwai cikakkiyar karramawa ta soji.

A wani labarin kuma, Shugaban Hukumar Kula da “Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutarez yace rundunar kiyaye zaman lafiya ta hadin guiwar Kungiyar Taraiyar Africa da Majalisar Dinkin Duniya, ba zata iya samar da tsaro ga yankin Darfur ba, sai an sami wata yarjejeniyar zaman lafiya.

Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke samar da kayan jin kai ga mutum miliyan biyu da rabi da yakin Darfur ya raba da muhallinsu, tayi kashedin cewa yanayin tsaro na kara tabarbarewa a sansanonin ‘yan gudun hijira. Antonio Gutarez, ya roki kasashen duniya da su tilastawa Gwamnatin Kasar Sudan da ‘yan tawayen kasar, su dauki matakan cimma yarjejeniyar zaman lafiya, idan aka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu, a karshen wannan watan.

A shekara mai zuwa ake sa ran rundunar hadakar Kungiyar Tariyar Africa da Majalisar Dinkin Duniya zata fara aiki a Darfur, a yayin da aka sanya 27 ga watan nan na Octoba ta zama ranar da za a gudanar da wani zagayen taron sulhun a kasar Libya, a matsayin wata hanya ta kwantar da hankula kafin isowar dakarun. Wasu daga cikin ‘yan tawayen sunce ba zasu halarci taron ba.

XS
SM
MD
LG