Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Janaizar Sojojin Najeriya Da suka Mutu a HAdarin Mota Ranar Laraba


Shugaban Najeriya Umar Musa Yar’adua, ya jagoranci jana’izar sojojin Najeriya arba’in da shida da suka mutu a hadarin mota kan hanyar su ta komawa sansanin su dake Jihar Borno,ranar Laraba.

Cikin jawabin sa Shugaba Umar ‘Yar’adua yayi alkwarin Gwamnatin sa zata yi bakin kokarin ta wajen tallafawa iyalan mamatan.

Anyi jana’izar ce a a makabartar kasa dake Abuja.Manyan jami’an Gwamnati da dama ciki harda iyalan sojojin ne suka halarci jana’izar.

XS
SM
MD
LG