Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-moon Zai Ziyarci Kwango


Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya, Ba Ki-moon zai sauka a birnin Nairobin Kenya a yau Juma’a, domin halartar wani taro da zai tattauna matsalar Jamhuriyar Kwango ta Kinshasa.

Ana sa ran Shugaban Kwango, Joseph Kabila zai halarci taron, tare da takwaransa na Rwanda Paul Kagame, da wasu shugabannin kasashen Afirka biyar.

Jami’ar Diplomasiyyar Amurka, Jendayi Frazier wata kwararriya a kan harkokin Afirka, ita ce zata wakilci Amurka a wajen taron.

A jiya Alhamis Ban Ki-moon yayi kiran da a gaggauta tsagaita wuta a fadan da ake fafatawa a gabashin kasar tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawaye, wanda yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam, Human Rights Watch ta fada a jiya Alhamis, cewa an kashe mutum 20, a yakin da suke domin kame kauyen Kiwanja. Kungiyar tace dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisr Dinkin Duniya in banda kallo babu abin da suke tabukawa.

XS
SM
MD
LG