Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Da John McCain Sun Hadu Sunyi Barkwanci


‘Yan takarar shugabancin Amurka, John McCain na jam’iyyar Republican da Barack Obama na Democrat sun ci gaba da yakin neman zabe a jihohi masu muhimmanci, kwana daya da gudanar da muhawara ta karshe a tsakaninsu.

A wani taron gangami da ya gudanar a jihar New Hempshire, Sanata Obama ya zargi Sanata John McCain da kaddamar da kamfe na bata suna, a lokacin da suka yi muhawara a jiya, maimakon ya maida hankali kan al’amura masu muhimmanci kamar na tattalin arziki.

A wannan muhawara dai, John McCain ya yiwa Obama zarge-zarge, sannan yayi watsi da kokarin Obama na alaknta shi da gwamnatin Republican ta Shugaba Bush.

A nasa taron gangamin, Sanata McCain yayi alkawarin samawa Amurka sabuwar alkibla.

Da yammacin jiya kuma ‘yan takarar biyu sun halarci wata liyafar cin abincin dare, wadda Gidauniyar Tunawa da Alfred Smith, kan shirya ko wacce shekara a birnin New York.

‘Yan takarar sunyi amfani da taron wajen barkwanci tsakaninsu, inda suka rika tsokanar juna. Liyafar da kan tara gudunmawa domin bada tallafin magunguna ga mabukata, ita ce ta sittin da uku.

XS
SM
MD
LG