Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birnin Washington Ya Dinke Da Jama’a


Tun kimanin karfe hudu na asuba, lokacin Washington mutane suka rika tururuwa daga sassa jihohin Maryland da Virginia, masu makwabtaka da Washington, suna shiga jiragen kasa domin su halarci wannan taro da za a fara da misalin karfe goma na safe. Ko wacce tashar jiragen kasa, ta cika makil da jama'a, yawancinsu dauke da na'urorin daukar hoto, da suka fara daukar hotuna tun kafin ma su isa wurin gudanar da bikin.
Ko ina mutum ya duba, sai walkiya kawai ake ta gani, ko dai ta hasken kyamarori masu daukar hoto, ko kuma na fitilun motocin jami'an tsaro. Birnin na Washington da aka sanshi a matsayin kurman gari, ya sauya yanayi a yau, inda ya dau haske, ga mutane suna ta hada-hada.Tun karshen makon jiya kuma aka rika gudanar da tarukan walima a bangarori dabam-dabam na birnin.

Ko a daren jiya ma saida Shugaba Barack Obama ya jagoranci walima domin karrama wadansu hanshakan mutane guda uku – Janar Collin Powell, wani fitaccen bakar fatar Amurka wanda Amurkawa ke girmamawa, sai Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden, sai kuma Sanata John McCain, dan takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar Republican, wanda Barack Obama ya kayar. Wannan shine karon farko da Shugaban Kasa yake karrama abokin adawarsa da ya kayar, a tarihin siyasar Amurka.

Da karfe goma sha biyun rana, za a rantsar da sabon Shugaban Kasar a matattakalar Majalisar Amurka ta Capitol, a kan idon mutanen da yawansu bai gaza miliyan biyu ba. Daga baya kuma za a yi gagaruminm Faretin masu kayan sarki, da nuna kayan tarihi da al'adun Amurkawa.

Batun tsaro kuwa, an dauki tsauraran matakai, inda aka rufe kusan dukkan hanyar da ta doshi tsakiyar Washington. a matattakalar Majalisar Amurka ta Capitol, a kan idon mutanen da yawansu bai gaza miliyan biyu ba. Daga baya kuma za a yi gagaruminm Faretin masu kayan sarki, da nuna kayan tarihi da al'adun Amurkawa.

Batun tsaro kuwa, an dauki tsauraran matakai, inda aka rufe kusan dukkan hanyar da ta doshi tsakiyar Washington. Kazalika gadoji da hanyoyin da suke shiga Washington daga makwabtan jihohi, duk an rufe su, babu mai shiga sai motocin jami'an tsaro da na ma'aikatan gaggawa, da kuma masu tafiya a kafa. Hukumomi sun bukaci jama'a da suyi amfani da jiragen kasa wajen zirga zirga a birnin, har zuwa lokacin da za a kammala bukukuwan.

XS
SM
MD
LG