Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indiya Ta Bukaci Pakistan Ta Mika Mata Sama Da Mutane Ashirin Da Take Zargi Da Ta'addanci.


Ƙasar India ta bukaci Pakistan ta miƙa mata sama da mutane 20 da ake zargi da ayyukan ta’addanci waɗanda ake kyautata zaton suna samun mafaka a Pakistan.

Ministan harkokin ƙasashen ƙetare na ƙasar India Pranab Mukherjee ya shaidawa manema labarai cewa an gabatar da wannan bukatar ne a cikin wasiƙar da jakadan ƙasar Pakistan a India yayin wani zama da aka yi jiya Litinin. Akwai Dawood Ibrahim a cikin jerin sunayen, wanda ake zargi da kitsa kai harin bom a Mumbai cikin shekara ta dubu da ɗari tara da casa’in da uku wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 250.

India ta nemi a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kan waɗanda suke da hannu a harin da aka kai makon jiya a birnin Mumbai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 175 da suka haɗa da ’yan ƙasashen ƙetare 18. Mukherjee yace India bata da niyar ɗaukar matakin soji kan Pakistan sakamakon wannan harin.

XS
SM
MD
LG