Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Yayi Ban Kwana Da Washington


Shugaba George W. Bush yayi ban kwana da fadar White House a matsayinsa na Shugaban Amurka.

Mr Bush da uwargidansa Laura sun halarci wajen rantsar da Shugaba Barack Obama, wanda ya gaje shi.

Tun da safe saida Mr. Bush da uwargida Laura, suka karbi Shugaba Barack Obama da uwargida Michelle a fadar White House, inda suka yi karin kumallo tare, daga inda suka wuce harabar Majalisar Dokoki kai tsaye domin bikin kaddamarwar.

Mr. Bush ya bar ofis da mafi karancin tagomashi da wani Shugaban Kasa mai barin gado ya taba fuskanta a tarihin siyasar Amurka.

Bayan kammala bukukuwan rantsuwar, iyalin na Bush sun shiga jirgi mai saukar ungulu, zuwa filin jiragen saman Dakarun saman Amurka na Andrews, dake nan bayan garin Washington, inda za a yi masa bukukuwan ban kwanan kafin ya tashi zuwa Texas.

Kafin ya bar ofis, saida tsohon Shugaba Bush ya barwa Shugaba Obama wata takarda kan teburinsa dake ofishin shugaban kasa. Kakakin Shugaba Bush Dana Perino tace Mr. Bush ya bar takardar a cikin aljihun teburin a jiya da dare. Saidai bata yi bayanin abin da takardar ta kunsa ba.

Mr. Bush zai halarci wani bikin yi masa maraba da dawowa gida a kauyensu na Midland, Jihar Texas, kafin ya zarce zuwa gidan gonarsa dake Crowford. Daga karshe dai Bush da uwargidansa zasu koma Dallas, bayan kammala 'yan gyare-gyare.

XS
SM
MD
LG