Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buzaye Sun Sace Jakadan Canada A Nijar


Wata kungiyar buzaye ‘yan tawaye a Jamhuriyar Nijar, tace ita ce ta sace wani wani jami’in diplomasiyyar kasar Canada, wande ke yiwa Majalisar Dinkin Duniya aiki.

Kungiyar FFR mai da’awar kare martabar al’umma, ta buga a dandalinta na yanar gizo yau, cewa ita ce ta kame Robert Fowler da wasu mutane uku a jiya Litinin.

Shugaban kungiyar ta FFR, Rhissa Ag Boula ya baiyana cewa jami’in diplomasiyyar yana cikin kopshin lafiya, kuma nan ba da dadewa ba za a mayar da shi wani wurin da za a fi samun tsaron lafiyarsa sosai.

Majalisar Dinkin Duniya tace Fowler shine jakadan ta na musamman a Jamhuriyar Nijar. Jami’ai suka ce an sami motar da Fowler tare da wami ma’aikacinsa da direbansa suke ciki, an yasar da ita ranar Lahadi, kimanin kilomita hamsin daga babban birnin kasar na Yamai.

XS
SM
MD
LG